Laraba 29 Afirilu 2026 - 21:30
Kada Mu Nemi Yardar Maƙiya / Masu Girman Kai Ba Za Su Gamsu Ba Sai Mun yi Bankwana da Musulunci

Hauza/ Ayatullah al-Uzma Makarim Shirazi ya jaddada cewa masu girman kai na duniya ba za su daina cutar da musulmi ba, kuma duk lokacin da musulmi suka ja da baya da taku guda, su kuma suna matsawa gaba da wani taku gudan. Ya ce: "za su gamsu da mu ne kawai idan muka yi bankwana da Musulunci."

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, Ayatullah Makarim Shirazi a cikin amsarsa ga wannan muhimmiyar tambaya cewa: “Dangane da ayoyin Alƙur’ani mai girma, yaushe rikicin da ke tsakanin masu girman kai na duniya da musulmi zai ƙare?” ya bayyana cewa: "kamar yadda Allah Madaukaki ya ce game da Yahudawa da Nasara: “Yahudawa da Nasara ba za su taɓa yarda da kai ba sai ka bi addininsu.” Saboda haka masu girman kai na duniya ma ba za su daina cutar da musulmi ba, kuma duk lokacin da musulmi suka ja da baya da taku (taƙi)guda, su kuma suna matsawa gaba da wani takun guda. Hakika za su gamsu da mu ne kawai idan muka yi bankwana da Musulunci."

Wannan babban marja'in addini ya tunatar da cewa masu girman kai na duniya ba za su daina tsangwama da cutar da musulmi ba. Duk lokacin da musulmi suka ja da baya da taku guda, su kuma suna matsawa gaba da wani takun guda. Za su gamsu da mu ne kawai idan muka yi bankwana da Musulunci. Kamar yadda Allah Madaukaki ya ce a aya ta 120 a Suratul Baqara:

 «وَ لَنْ تَرْضَی عَنْکَ الْیَهُودُ وَ لاَ النَّصَارَی حَتَّی تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ»

Ma’ana: “Yahudawa da Nasara ba za su taɓa yarda da kai ba sai ka bi addininsu.”

Saboda haka bai kamata mu nemi yardarsu ba; abin da ya wajaba gare mu shi ne mu yi abin da ya rataya a wuyanmu.

Har ila yau ya jaddada cewa kasarmu (Iran) ta iya jurewa takunkumi da matsin lamba. Hatta a batun makamashin nukiliya ma, imani da akida da jarumtakar matasa ne suka kawo mafita. Idan ma makiya ba su amince da bukatunmu ba kuma ba a cimma wata yarjejeniya ba a batun nukiliya, har yanzu za mu iya kasancewa “masu nasara a filin gwagwarmaya.”

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha